
*MUSULUNCI SHINE DARAJA TA.*
-
"Da zuwan musulunci sai ya bawa dukkanin wani ɗan adam cikakken ƴa'ncinsa, saɓanin yadda maguzanci yake tauye haƙƙin mutane musamman ma mata, an ɗauke su tamkar wasu bayi waɗanda basu da ƴa'ncin rayuwa"
-
"Sabida tsabar sun tsani matan ma, basa so suji matayensu na gida sun haifa musu ƴaƴa mata, idan kuwa aka yiwa ɗaya daga cikinsu busharar samun ɗiya mace, sai ya ɓata rai ya fara tunanin shine zai riƙeta cikin muzantawa ne ko kuma dai kawai yaje ya binne ta acikin rami? Kai tir da wannan hukunci da suke yankewa"
-
"A zamanin jahiliyya mata basu da daraja basu da ƙima, kullum suna cikin rayuwar ƙasƙanci, sun ɗauki mace tamkar wata dabba wacce saidai suyi amfani da ita su watsar, sun danne mata haƙƙoƙinta, sabida tsabar ƙasƙanci ma, idan mahaifi ya rasu, sai babban ɗansa ya gaji dukkanin ilahirin matayensa yayita kwanciyar aure dasu kamar yadda mahaifin nasa yayi, matan da suke a matsayin iyayensa, amma duhun jahilci da maguzanci ya halatta masa ƙazamar kwanciya dasu, amma da musulunci yazo, sai ya kori wannan al'adar, ya kuma bawa mata ƴa'nci irin wanda basu taɓa samunsa a baya ba, Allah mun gode maka abisa ni'imar musulunci"
0 Commentaires